Hannatu Musa Musawa, Wadda Ta Fito Daga Jahar Katsina Ta Fashe Da Kuka A Yayi Da Ake Kokarin Tantance Ta Domin Zama Minister A Gwamnatin Bola Tinubu, Ranar Talata A Majalisar Dattawan Najeriya. Ta Bada Labarin Yadda Mahaifinsu Ya Taso Talaka Me Tallan Goro, Daga Baya Ya Kokarta Ya Samu Ilimin boko.
Ganin Mahaifinta Alhaji Musa Musawa Ya Rasu Saura Watanni 4 A Za6eta A Matsayin Minister A Tarayya Najeriya, Hakan Yasa Ta Fashe Da Kuka 😭Da Hawaye A Gaban Al’umma A Majalisar Tarayya.
Hannatu Ta Kara Da Cewa Taso Ace Mahaifinta Yana Da Rai Yaga ‘Yarsa Ta Zama Minister, Saboda Sun Taso Ne A Cikin Tsananin Talauci. Akwai Darussa Da Yawa Wanda Yakamata A Labarin Wannan Sabuwar Minister
إرسال تعليق