Amfani 10 da karas ke yi a jikin dan adam:
Idan kina so har ki tsufa Mijin ki yana jin dadin matsa nonon ki, kalli video domin ganin yadda ake today is my birthday
January 7, 2023
SAURIN INZALI (PREMATURE EJACULATION)
March 27, 2023
Yadda Ake Gyaran Kafa Na Musamman (kaushi ko faso
February 27, 2023
🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕
Binciken kimiyya ya bayyana cewa bayan karin dandano da karas yake karawa abinci yana kuma dauke da sinadarai masu yawa da suka hada da antioxidants, beta-carotene, alpha-carotene, lutein, potassium, vitamin C, vitamin A, fibre da Carotenoids.
A sakamakon wannan sunadarai da karas ya kunsa, ga cututtuka takwas da yake kawarwa:
1. Taimakawa wurin kiyaye kamuwa da ciwon daji (kansa):
Karas na dauke da sinadarai masu yawa da masana ke kira ‘Phytochemicals’ da ke yaki da cutan daji. Wasu daga cikin sinadaren sun hada da beta-carotene da sauransu.
Wadannan sinadaren na karfafa garkuwar jiki.
🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕🥕
Masana sun kuma gano karas na iya maganin Leukemia da kare yiwuwar kamuwa da ciwon daji na baki.
2. Inganta Lafiyar Ido Sinadarin Vitamin A yana taimakawa idanu su rika gani tangaran kuma karas na dauke da Vitamin A masu yawa. Idan mutum ya rasa Vitamin A na lokaci mai tsawo, yana iya fara samun da ganinsa.
3. Gyara fatan jiki Karas na dauke da sinadarai masu yawa da ake kira ‘carotenoids’. Binciken kimiyya ya nuna cewa ‘ya’yan itatuwa da ganye suna dauke da sinadarai na ke inganta lafiyar mutum ya kuma haskaka fatarsa ya.
Sai dai cin karas din fiye da kima yana iya haifar da matsala mai suna ‘carotenosis’ da ke saka fatar mutum tayi haske da yawa.
4. Bugun Zuciya Wani sabon bincike da masana kimiyya suka gudanar ya nuna cewa ruwan da aka tatsa daga karas na rage hawan jini da kashe 5 cikin 100. Sinadaren da ke cikin karas da suka hada da fibre, potassium, nitrates da Vitamin C ne ke taimkawa wurin wannan.
5. Taimakawa masu ciwon suga Cin abinci mai inganta lafiya yana taimakawa wurin rage kiba da kuma hana kamuwa da ciwon suga nau’i na biyu. Bincike ya nuna cewa Vitamin A na kare afkuwa da kamuwa da ciwon suga kuma tunda karas na kunshe da sinadarin sosai yana iya taimakawa.
Post a Comment