Allah Sarki Wannan Shine Tsohon Mijin Jaruma Sadiya gyale Marigayi Alhaji Abubakar Muhammad Wanda ya rasu a Kasar Turkiyya.






tsohon mijin Sadiya Gyale, wato Alhaji Abubakar Muhammad, rasuwa. Ya rasu a birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya a ranar Litinin ɗin wannan makon.

Wata majiya ta faɗa wa mujallar Fim cewa Alh Abubakar, wanda babban ɗan kasuwa ne, ya rasu sakamakon ciwon hawan jini da ya kama shi, kuma ya rasu jim kaɗan bayan an kai shi asibiti.

Majiyar ta ce ya je Istanbul ne harkar kasuwancin sa kamar yadda ya saba, to sai Allah Ya yi ƙarshen tafiyar kenan. A cewar majiyar, an tsara cewa za a kawo gawar sa Abuja daga Turkiyya ɗin washegari, wato Talata.

Allah Ubangiji Ya gafarta Masa Ameen

Post a Comment

Previous Post Next Post